Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kira ga tsayar da sallah da koyar da ita, da bayyana ma’anonin da ke cikinta, da riko da ita, wani aiki ne na wajibi da ya rataya a wuyan hukumomin da’awar addini da malamai da ma’abuta addini. Dole ne a yi amfani da hanyoyin zamani domin watsa wannan fanni.
A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike ga zaman taron cibiyar karfafa tsayar da sallah karo na 32 ya bayyana cewa: Taron karfafa tsayar da sallah yana daya daga cikin mafi fa’ida a tsakanin al’ummar kasa, kuma ranar da ake gudanar da ita tana daya daga cikin ranaku masu albarka a wannan shekara. Wannan ya samo asali ne daga kebantuwa da fifikon wannan wajibi na Musulunci mai ma’ana da muhimmanci.
Jagoran ya kara da cewa: Idan ana yin sallah da ladubban da suka dace, kamar tawali’u da mika wuya ga Allah, takan kwantar da zuciya, da karfafa niyya, da zurfafa imani, da rayar da fata. Kyakkyawar makomar mutum a duniya da lahira ta dogara da irin wannan zuciya, irin wannan wasiyya, da imani, da irin wannan fata. Don haka shawarar yin tsayar da sallah a cikin Alkur’ani da sauran nassosin addini ta fi kowace nasiha muhimmanci, don haka ake ganin cewa ita ce mafificiyar dukkan ayyuka a fagen addini.