Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar da martani mai tsanani.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Juma’a dangane da bikin sabuwar shekara ta Noruz a Husainiyyar Imam Khumaini dake nan Tehran, ya bayyana cewa; Babban kusakuren ‘yan siyasar Amurka da kuma na Turai , shi ne daukar ‘yan gwagwarmaya a wannan yankin da cewa ‘yan koren Iran, da hakan batunci a gare su.”
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kara da cewa; Al’ummar Yemen, kamar sauran ‘yan gwgawarmaya a cikin wannan yankin suna da dalilai na gwgawarmaya, Iran kuwa ba ta da bukatar ‘yan kore.”
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma kara da cewa; “Ko kadan, ba mu ne farau ba acikin wannan rikicin,amma idan wani ya fara aikata wani abu mummuna, to zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.
Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce; Karshen abinda zai faru da gwgawarmaya shi ne cin kasar abokan gaba ‘yan sahayonoya.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniya marasa rahama suke yi,ya sosa zukatan al’ummu musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya yi bitar muhimman abubuwan da su ka faru a shekarar da ta gabata ta hijira shamshiyya da su ka hada mai daci da kuma dadi. Daga ciki ya bayyana hatsarin da faru a wurin hako ma’adanai na Tabas, dake arewacin Iran, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50.