Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron kas ana raya salla karo na 32, ya yi ishara da rawar da sallolin farilla suke takawa wajen ayyana makomar mutum a duniya da kuma lahira. Haka nan kuma ya ce; Nauyi ne da ya rataya a wuyan cibiyoyin addini, da malamai da masu riko da addini da su rika yada yin kira da a yi salla da kuma bayyana sauyin da take samarwa a badinin mutum.
Bugu da kari jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya yi kira da a yi amfani da dukkanin hanyoyin sadarwa na zamani domin isar da wadannan sakwannin akan salla.
Sakon na jagora ya bayyana taron shekara-shekara da ake yi akan salla da cewa, yana cikin mafi muhimmanci da amfani a kasar, kuma ranakun dake gudanar da shi masu albarka ne.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma kara da cewa; Ayyana yin taro akan salla yana nuni ne da kasantuwarta wata farilla mai cike da tarbiyyar ruhi da bai wa rayuwa cikakkiyar ma’ana.
Jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; Iyaye maza da mata, sannan malamai da abokan zama duk suna da rawar da za su taka wajen koyar da salla ga matasa.