Search
Close this search box.

Iyalan Yahudawa Sun Bullo Da Salon Neman Yantar Da ‘Yan Uwansu Daga Hannun Falasdinawa

Iyalan fursunonin haramtacciyar kasar Isra’ila suna gudanar da wani yunkuri don samun tausayawar jama’a da kuma nuna adawa da Netanyahu Kungiyar iyalan fursunonin yahudawa da

Iyalan fursunonin haramtacciyar kasar Isra’ila suna gudanar da wani yunkuri don samun tausayawar jama’a da kuma nuna adawa da Netanyahu

Kungiyar iyalan fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Zirin Gaza ta “Forum for Families of Israel’ a jiya Laraba ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda aka kame wasu sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila mata da dama daga sansanin sojan Nahal Oz, yayin kai harin Dakarun Izzuddeen Al-Qassam a ranar 7 ga watan Oktoba, a wani yunkurin da suka yi don samun nuna jin kai na al’umma da kuma jaddada adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu don matsawa matsa mata kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas.

Bidiyon ya kuma nuna yadda aka kama wasu mata masu sa ido a cikin sojojin haramtacciyar kasar ta Isra’ila, kuma bidiyon ya kasance tare da wata sanarwa da ke neman al’ummar yahudawan sahayoniyya da su duba idanunsu kuma su lura da cewa an watsa faifan bidiyon ne da amincewar iyalan sojojin mata da suka bayyana a cikinsa. A cewar sanarwar, a wannan rana an kashe mata sojoji 15 a cikin sojojin mamaya a cikin sansanin Nahal Oz, yayin da aka kama masu sa ido mata 7 da ransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments