Majiyar tashar talabijin din al’mayadin ta ce, ‘yan mamaya suna ci gaba da rushe gidajen falasdinawa a yammacin Kogin Jordan da kuma birnin Kudus.
A safiyar yau Laraba ne dai jami’an tsaron mamayar su ka kai hari a garin Jabal-al-Mubakkir, tare da rushe wani gida kusa da shingen Sheikh Sa’ad.
Haka nan kuma motocin buldoza na ‘yan mamaya sun rushe wasu gine-gine a garin Kafar da kuma sansanin Kalandiya a arewa da birnin Kudus.
A arewa maso yammacin Nablus kuwa ‘yan mamayar sun rushe gidan iyalan Shahid Malik Salim dake garin Bazariya.
Hukumar agaji ta “Red-crecent” a Nablus ta bakin shugabanta Amid Ahmad, ta ce, harin na ‘yan sahayoniya ya jikkata wata mace daya yar shekaru 45 a lokacin da su ka yi kokarin kutsawa cikin sansanin ‘yan hijira na Askar.
Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kame Falasdinawa 5 a cikin yankunan mabanbanta na gudunar Bethlaham.
A daren jiya ‘yan share wuri zauna sun kai hari akan wani gida dake ynakin Dadi-Ajshaih a kusa da birnin al-khalil tare da fasa gilashan gida da kuma yanke dabbobin da suke ciki.
A cikin kwanakin bayan nan ne dai ministan yakin HKI Yisrael Katz ya ce, tun sun shimfida ikonsu a yammacin kogin Jordan.
A bisa kudurorin MDD, yankin yammacin Kogin Jordan ne aka bai wa Falasdinawa domin kafa daularsu. Sai dai gine-ginen da ‘yan sahayoniyar suke yi na matsugunan ‘yan share wuri zauan, ba zai bayar da damar hakan ba.