Bayanai daga Yemen na cewa jiragen Yakin Isra’ila sun kai hari a filin jirgin saman Sanaa da wasu wuraren da ‘yan Houthi ke rike da su.
An kai hare-hare ta sama a wurare da dama a kasar Yemen a ranar Alhamis din ann, ciki har da filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Sanaa da wata cibiyar samar da wutar lantarki, a cewar shaidu da kuma masu tayar da kayar baya.
Tashar talabijin ta Al-Masirah ta rawaito hare-harenna Isra’ila.”
A nata bangaren, Isra’ila, ta tabbatar da kai hare-haren kan abinda ta danganta da “makamai na soji” na Houthis.
Hare-haren dai na zuwa ne bayan wani sabon harin makami mai linzami da aka kai kan Isra’ila a makon jiya, wanda ‘yan Houthi suka yi ikirarin cewa na goyan bayan al’ummar Gaza ne da Isra’ila ke zalinta.
Tun lokacin da aka fara yakin Zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ‘yan Houthis sun kaddamar da hare-hare da dama kan Isra’ila, suna masu ikirarin goyan bayan Falasdinawa.