Rundunar sojin Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a kusan makarantu 21 da ke mafaka ga dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a zirin Gaza tun watan jiya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 267 tare da jikkata wasu daruruwa, in ji kungiyoyin kare hakkin bil’adama.
Akalla Falasdinawa 22 ne suka mutu da sanyin safiyar Asabar a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka farmawa wata makaranta da ke dauke da fararen hula da ke zaune a unguwar Zeitoun da ke birnin Gaza, a cewar hukumomin yankin.
Ofishin yada labarai na gwamnati ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wadanda aka kashe a “mummunan kisan ” na Isra’ila sun hada da yara 13, mata 6, da kuma jariri dan watanni uku.
Akalla mutane 30 ne suka jikkata, in ji ma’aikatar lafiya, ciki har da wasu da dama da suka kone.
A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Med, wata kungiyar kare hakkin bil adama da ke da hedkwata a Geneva, harin “sabon laifi ne da za a kara da shi cikin jerin laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza.”