Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa hukumar tsaron cikin gidan gwamnatin sahyoniyawan ta kafa wata runduna ta musamman ta sirri domin kashe Yahya Sinwar, magajin Shahid Haniyeh.
Tashar Talabijin ta Isra’ila ta 12 ta bayyana cewa hukumar (Shin Bet) ta ware makuden kudade domin samun damar kashe Yahya Sinwar, sabon shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta (Hamas).
Tashar ta bayyana cewa : Tun bayan da aka fara yakin Gaza, hukumar ta kafa wata runduna ta musamman ta leken asiri, wadda ke da alhakin sa ido na tsawon sa’o’i 24 na yunkurin kasha sabon shugaban kungiyar Hamas.
Majiyar kafar yada labaran Isra’ila ta kuma yi ikirarin cewa:
Sinwar bai amfani da wayoyin hannu ko na’urorin sadarwar lantarki ba, Amma yana amfani da cibiyoyin sadarwa da dama don gudanar da ayyukan soja na Hamas.
“Duk kokarin da sojojin Isra’ila sukayi na kashe Sinwar, yana bacewa a duk lokacin da sojojin suka iso,” a cewar kafar yada labaran.