Search
Close this search box.

Isra’ila Na Ci Gaba Da Kashe Falastinawa A Gaza Da Gabar Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa 12 a jerin hare-hare a yankin Gaza da aka mamaye, yayin da aka zaƙulo wasu gawawwaki daga wuraren da sojojin

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa 12 a jerin hare-hare a yankin Gaza da aka mamaye, yayin da aka zaƙulo wasu gawawwaki daga wuraren da sojojin Isra’ila suka bari, da suka yi ka-ka-gida a baya.

Mai magana da yawun Cibiyar Kare Fararen-Hula ta Falasɗinawa Mahmoud Basal ya bayyana cewa an kashe Falasɗinawa shida a wasu hare-haren Isra’ila biyu ta sama a Jabalia da ke arewacin Gaza, ciki har da wani hari da aka kai wa wani taron mutane.

A unguwar Sheikh Radwan da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza kuwa, an kashe wani Bafalasɗine a harin jirgin saman Isra’ila a wani gida da ake zama, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A tsakiyar Gaza ma, an kashe Falasɗinawa biyu a wani hari ta sama kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da kuwa wani wajen da jama’a suka taru a Deir al-Balah.

A Khan Younis kuma, Falasɗinawa uku aka kashe a wani hari ta jirgin yaƙi a kan wani gida a garin Abasan al-Kabira, a gabashin Khan Younis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments