Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta samo asali ne sakamakon jajircewa da tsayin daka da hadin kan al’ummar Falasdinu, wanda idan ba tare da hakan ba yarjejeniyar ba za ta taba cimma ruwa ba.
Bayan shafe sama da shekaru biyu ana kai hare-hare ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan Falasdinawa, gwamnatin Isra’ila bisa matsin lambar kasa da kasa ta amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla na kawo karshen yakin da take yi a zirin Gaza da kuma musayar fursunoni da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa, inji Islamic Jihad.
A matakin farko na yarjejeniyar da ta fara aiki ranar Juma’a, Hamas ta sako wasu ‘yan Isra’ila 20 da tayi garkuwa da su, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen mika gawarwakin wasu 28 na daban.
A maimakon haka, Isra’ila ta saki Falasdinawa kusan 2,000.
Falasdinawan da aka saki sun hada da kusan 1,700 da Isra’ila ke rike da su ba tare da tuhumar su ba tun watan Oktoban 2023 da kuma wasu 250 da ke daurin rai da rai.
Ofishin yada labarai na fursunonin Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, 154 daga cikin wadanda aka sako an tilasta musu yin gudun hijira a Masar.