Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( Irgc), sun sanar da cewa; muna cikin Shirin ko-ta-kwana domin gabatar da salin yaki mai cike da mamaki wanda abokan gaba ba za su iya fahimtarsa ba.”
Bayanin na dakarun kare juyin musuluncin ya kara da cewa; Iran tana da wasu sabbin salon yakin da ya zuwa yanzu ba su yi amfani da su ba.
Sanarwar ta zo ne a yau 2 ga watan Farvardin da ita ce ranar dakarun kare juyin musulunci da ake yin bikinta a kowace shekara, inda su ka jaddada cewa;
“Tarihin shekaru 48 na dakarun kare juyin musulunci ta Iran yana cike da ci gaba mai yawa, a fagage mabanbanta, da kuma dakile makiricn makiya da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke son karkatsa kasa.”
Bayanin ya kuma ce; Tun a lokacin da juyin musulunci yake jariri har zuwa shekaru 8 da su ka biyo baya na tsaron kasa mai tsarki a gaban masu girman kai na duniya dakarun kare juyin musuluncin na Iran sun dakile duk wani makirci,kamar yadda a yanzu a wannan tsaron kare kasa mai tsarki na uku suke takawa masu wuce gona da iri birki cikin nuna karfi.