Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) ya ce “A kowace rana ana dada sabunta makamai masu linzami na kasar ta fuskar adadi, inganci.”
Laftanar Janar Hossein Salami, na magana ne game da abubuwan da ke faruwa na baya-bayan nan a yankin, musamman jita jitar cewa an raunana karfi da ikon Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
“A yau za mu iya harba daruruwan makamai masu linzami a lokaci guda, sama da 200 cikin nasara su cimma burin da ake so inji shi.
Babban kwamandan dakarun IRGC ya jaddada cewa al’ummar Iran sun tsaya tsayin daka wajen yakar makiya da hannayensu.
“Ba mu taba dogaro da wani taimako daga waje don kare ‘yancin kanmu.
Janar Salami ya kara da cewa: “Muna so mu gaya wa makiyanmu cewa su yi tunani da kyau a kan lissafinsu, kada su yi kuskure kuma su yi taka tsantsan, Saboda Ba za mu yi rangwame ba. »