Kamfanin man fetur da gas na kasar Iran zai fara aikin nema da hakar man fetur a tekun Caspian da ke arewacin kasar, wanda mataki ne na ci gaba ga kamfanin musamman a halin da ake ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an kamfanin na cewa tuni sun kai kayakin aiki zuwa wuraren da suke zata akwai danyen man fetur a cikin tekun, sannan a shirye suke su fara aiki don hakar man daga yanzun.
Ba wannan ne karon farko wanda gwamnatin kasar Iran take hakar danyen man fetur a cikin tekun Caspian ba, saboda a shekara ta 1997 ne ta dakatar da hakar mai daga gabar tekun, sannan ta dakatar da hakar man a tsakiyar tekun a shekara ta 2014.
Labarin ya kara da cewa ministan man fetur na kasar ne Mohsen Paknejad ya kaddamar da aikin hakar man a gefen kasuwar baje koli na Gas, tashewa, da sinadaran danyen mai karo 29 da ke gudana a nan tehran.