Iran Zata Ci Gaba Da Kare Shirinta Na Makamashin Nukliya Da Duk Karfin Da Take Da Shi: Ali Shamkahani

Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran za ta ci gaba da

Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran za ta ci gaba da kare shirinta na makamashin Nukliya na zaman lafiya da duk karfin da take da shi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ali Shamkhani ya na fadar haka, a lokacinda ya ziyarci wata kasuwar baje koli,  inda cibiyar makamashin Nukliya ta kasar Iran (AEOI) ta ke baje kolin irin ci gaban da ta samu a wannan fasahar a yau litinin a nan Tehran.

Babban mai bawa jagora shawara a kan al-amuran siyasa ya kara da cewa, gwamnatin JMI za ta ci gaba da kare duk abinda zai amfani mutanen kasar Iran, ko da kuwa manya-manyan kasashen duniya basa son hakan.

Ya ce, JMI bata da manufar kera makaman nukliya a yanzu ko nan gaba, amma fasahar nukliya tana da matukar muhimmaci, a fannonin ilmi da dama, daga ciki, har da samar da magunguna, ayyukan noma, makamashin lantarki mai tsabata, wanda baya gurbata yanayi, samar da ruwa, da kuma gyra yanani da sauransu.

Ali Shamkhani ya kammala da cewa, Don haka duk tare da adawar da wasu manya-manyan kasashen duniya suke nunawa iran kan mallakar wannan fasahar, ba za ta taba barin ta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments