Kasar Iran zata ci gaba da dagewa a fagen mara wa Siriya baya wajen tunkarar sabuwar makarkashiyar cuna mata ‘yan ta’addanci
Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ta bakin manyan jami’anta, ta tabbatar da goyon bayanta na din din din a fagen tallafawa kasar Siriya wajen fuskantar ta’addanci da makirce-makircen da ake kullawa kanta tare da mafi girman goyon baya da taimako.
Bullar rikice-rikice ba su canza matsayi, kamar yadda kalubale baya girgiza ka’idoji da kyakkyawar azma…Don haka tarihin alaka da kyakkyawar abokantaka da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jamhuriyar Larabawa ta Siriya, ba zasu taba canzawa ba, kamar yadda ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da gwamnatin Siriya da sojojinta gami da al’ummar kasar, a wannan masifa da aka jarrabe su da ita ta sake cuno musu ‘yan ta’adda maras ruhin dan Adamtaka ko zurfin tunani.
Araqchi ya kuma jaddada cewa: Kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka shiga kasar Siriya a baya-bayan nan, suna samun goyon bayan Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila ne, wanda hakan ke bukatar daukar matakin gaggawa da kwararan matakai daga kasashen duniya. Yana mai jaddada cewa; Farfaɗo da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a Siriya ya zo ne daidai da sanarwar tsagaita wuta a Lebanon.