Iran : Zamu Mayar Da Martani Mai Tsanani Idan Isra’ila Ta Kawo Mana Hari

Iran ta ce zata mayar da martini mai tsanani muddin Isra’ila ta kuskura kai mata hari. Da yake sanar da hakan Ministan tsaron Iran ya

Iran ta ce zata mayar da martini mai tsanani muddin Isra’ila ta kuskura kai mata hari.

Da yake sanar da hakan Ministan tsaron Iran ya lashi takobin cewa kasar za ta yi wa gwamnatin Isra’ila “mummunan raddi” matukar gwamnatin kasar ta zabi mayar da martani kan matakin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauka a baya-bayan nan kan ayyukan wuce gona da iri na Tel Aviv.

“Idan gwamnatin sahyoniyawan ta kuskura ta mayar da martani, matakanmu na gaba za su yi tsanani sosai, kuma za mu tura wasu karin makamai masu linzami da muke da su,” in ji Birgediya Janar Aziz Nasir-zadeh.

“matakin da muka dauka daren jiya yana wakiltar wani bangare ne kawai na karfin makamai masu linzami na Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” in ji shi, ya kara da cewa, “Ba a yi amfani da wani bangare mai yawa na wannan damar ba tukuna.

Shi ma a nasa bangare Shugaban rundunar sojojin Iran ya sha alwashin kai hare-hare a dukkan kayayyakin Isra’ila a fadin kasar muddin aka kai musu hari.

Za a “kai manyan hare-hare masu karfi kan dukkan kayayyakin Isra’ila,” in ji Manjo Janar Mohammad Bagheri a jawabin da ya yi ta gidan talbijin.

Janar Bagheri ya jaddada cewa Iran za ta iya kai hari kan ababen more rayuwa na tattalin arzikin Isra’ila amma ta zabi ta kai hari kan sansanin sojin Isra’ila.

Bayannin na su dai na zuwa ne bayan da Iran ta kai hari da makamai masu linzami 200 kan Isra’ila, wacce take kisan kare-dangi a yankin Gaza da kai hare-hare a Lebanon.

Hare-haren na daren jiya Talata da Iran, ta ce martani ne kan kisan Ismael Haniyeh shugaban ofishin siyasa na Hamas a cikin kasarta da kuma shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah, tare da wani babban kwamandan rundinar IRGC, Abbas Nilforoushan a kudancin Beirut a ranar Juma’a data gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments