Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu.
Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa:
“ Za mu kara yawan wutar lantarkin da muke samarwa da megawati 2000 a kowace sa’a daya daga nan zuwa karshen zangon na bakwai na tsare-tsaren ci gaba da ake yi a kowace shekara 5. Zangon dai zai kare ne a cikn watan Maris 2029.
Salami ya ce za a kara megawati 1,000 a cikin kowace sa’a da hakan zai mayar da abinda ake samarwa zuwa megawati 3,000 a cikin kowace sa’a.