Iran Za ta Karbi Bakunci Taron Ministocin Cikin Gida Na Kungiyar ECO

Rahotanni sun bayyana cewa Tehran za ta karbi bakunci taron ministocin cikin gida na  kungiyar Eco a karon farko a cikin shekaru 15 da nufin

Rahotanni sun bayyana cewa Tehran za ta karbi bakunci taron ministocin cikin gida na  kungiyar Eco a karon farko a cikin shekaru 15 da nufin karfafa tsaro  da kuma kara fadada yin aiki tare a bangarorin tattalin arzik,i aladu, da kuma harkokin diplomasiya a yankin.

Jami’an iran sun tsinkayi irin alfanu da taron kwanaki 2 zai kawo da zai kunshi jerin tattaunawa tsakanin kasashen da sauran bangarori daban –daban.

Wannan taron yana zuwa ne lokacin da kasashen dake mambobi a kungiyar suke fuskantar kalubale , da suka hada da rashin tsaro a iyakoki, da aikata muggan laifuffuka da aka tsara, da kuma rashin zaman tabbas a yankin,

iran na nufin fadada ajendar ta hanyar yada aladu da amfani da diplomasiya a iyakokin da kuma samar da hadin guiwar tattalin arziki,  ganin cewa ma’aikatar harkokin cikin gida tana sa ido a iyakoki da shuwagabannin kanana hukumomi, kuma sun yi hadin guiwa tsakanin birane a matsayin wata hanya ta hadin guiwa a yankin, don samar da tsaro.

Ana sa bangaren kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida ta Iran Ali zeinivand ya fadi cewa taron minstocin harkokin cikin  gida na kungiyar Eco zai hada da tattaunawa tsakanin kasashe biyu da kuma na bangarori daban daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments