Search
Close this search box.

Iran: Yankin Yammacin Asiya Ba Za Ta Sami Zaman Lafiya Ba Sai Da Kawon Karshen Mamaya Da Kuma Kwance Damarar HKI

Iran ta bayyana cewa yankin Asiya ta yamma ba zata taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba sai bayan an kawo karshen mamayar da

Iran ta bayyana cewa yankin Asiya ta yamma ba zata taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba sai bayan an kawo karshen mamayar da akewa kasar Falasdinu, da kuma kwance damarar  makaman nukliya na HKI.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan yana fadar haka a jiya Lahadi a taron tattaunawa tsakanin kasashen larabawa da JMU karo na ukku wanda ake gudanarwa a nan Tehran.

Ministan ya kara da cewa an hana al-ummar Falasdinu dukkan hakokinsu, sannan yakin da HKI ta dorawa mutanen kasar a cikin watanni 7 da suka gabata sun nunawa duniya yadda aka maida su.

Ya ce HKI ta nuna cewa ba zata iya zama tare da wasu a yankin Asiya ta Kudu ba, a matsayin kasashe masu yenci, da haka kuma ta tabbatar da rashin zaman lafiya a yankin gaba daya.

Daga karshe ministan ya kammala da cewa shawarar JMI ita ce, dole ne a gudanar da zaben raba gardama a kasar Falasdinu, tare da halattar dukkan yan kasar wadanda suka hada da musulmi, kirista da yahudawa don su fayyace makomar kasarsu karkashin shugabanci guda.

Har’ila yau a wani wuri a jawabinsa Abdullahiyan ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta kyautata dangantaka da dukkan kasashen larabawa musulmi da kuma makobtanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments