Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata.
Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji, wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari.
Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman a matsayin wata hujja dake tabbatar da laifukan yaki da Amurka da Isra’ila suka tafka, kuma za ta bi dukkan hanyoyin doka wajen kare hakkin alummar iran.