Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaee ya yi kira ga kasashen duniya su gaggauta kawo karshen kisan kiyahsin da HKI take yi a Gaza, ya kuma kara da cewa shirun da kasashen duniya musamman kwamitin tsaro na MDD suka yi dangane da abinda ke faruwa a Gaza abin kunya ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar haka a yau Litinin. Ya kuma kara da cewa dole ne a kawo karshen kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza, a kuma hukunta wadansa suka aikata ko suka taimaka wajen kissan kare dangin da ke faruwa a Gaza.
Baghaie ya ce a mummunan hare-haren da HKI ta kai kan sansanin yan gudun hijira na Nusairat a baya-bayan nan, da kuma kan tentunan Falasdinawa a Nusairat, sun kashe fiye da Falasdinawa dozen guda. Sannan daga cikin wadanda suka kashe har da mata da yari.
Daga karshe jami’in diblomasiyyar ya kammala da cewa, wajibe ne ga kasashe 124 wadanda suka amince da kotun ICC su aiwatar da umurnin kotun na kama wadanda ake zargi da aikata laifuffukan yaki a HKI. Sannan dole ne sauran kasashen duniya su yi biyayya ga dokokin kasa da kasa kan hukunta wadannan masu aikata laifin.