Iran Tana Daukan Tattaunawarta Da Amurka Da Muhimmanci Dangane Da Shirinta Na Nukiliya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada muhimmanci game da tattaunawa da ita kuma a shirye take ta magance matsaloli da takaddamar da ake yi kan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada muhimmanci game da tattaunawa da ita kuma a shirye take ta magance matsaloli da takaddamar da ake yi kan Shirin makamashin nukiliyarta

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Kazim Gharibabadi ya bayyana cewa: zagayen farko na tattaunawar da ba na kai tsaye ba da aka gudanar a birnin Muscat na kasar Oman tsakanin Iran da Amurka, ba a samu wani babban sabani ba, kuma an yi shi ne domin tantance muhimmancin bangarorin biyu da kuma bayyana matsayinsu.

Gharibabadi ya kara da cewa: A wannan zagayen tattaunawan Iran ta nuna muhimmancin tattaunawar da kuma rashin son bata lokaci, yana mai cewa amincewa da shawarar da Amurka ta yi na gudanar da shawarwari ba wai saboda raunin Iran ba ne, sai dai abin da ya bayyana a matsayin karfinta da gazawar takunkuminta.

Gharibabadi ya tabbatar da cewa a ko da yaushe kasarsa a shirye take ta kawar da damuwar da ake da ita game da shirinta na makamashin nukiliya, yana mai jaddada cewa mallakar makamin nukiliya ba shi da wani matsayi a koyarwar tsaron Iran. Ya kuma yi nuni da cewa shirin inganta sinadarin uranium gaba dayansa na cikin gida ne, babu wata sabawa ka’ida, kuma ba zata tattaunawa kan tace sinadarin na uranium ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments