Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar.
Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen.
Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da kai hari kan kayayyakin more rayuwa na kasar domin daukar fansa kan hadin kan al’ummar Yemen da goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta.
Kakakin na Iran ya ce hare-haren na Amurka cin zarafi ne ga ka’idojin Yarjejeniya Ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma ka’idojin dokokin kasa da kasa.
Baghaei ya dorawa gwamnatin Amurka alhakin aikata laifuka.
Kafofin yada labaran kasar Yemen sun ruwaito a safiyar yau Juma’a cewa, an kai wasu sabbin hare-hare a babban birnin kasar Yemen, inda aka kai hari kan wani sansanin soji a kudancin Sana’a da wasu hare-hare guda hudu.
An kuma kai hare-hare a yankunan da ke kusa da filin jirgin sama na Sana’a, baya ga gundumomi biyu a kudanci da tsakiyar lardin Sana’a.