Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Kan Tsibiran Kasarta

Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya

Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa.

Isma’il Baqa’i ya tabbatar a jiya Litinin 19 ga watan Mayu cewa: Tsibiran nan uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa wasu bangarori ne na kasar Iran, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin duk wani da’awar a wannan fanni ya sabawa ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma keta mutuncin yankunan kasa da ka’idojin kasa da kasa a matsayin makwabciyar kasa. Yana ganin gabatar da irin wannan batu a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa ba abu ne da za a amince da shi ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya shawarci kungiyar kasashen hadin kan Larabawa da ta yi la’akari da tabbatattun hujjoji na tarihi da na kasa a lokacin da suke tsara matsayinsu, maimakon yin zarge-zargen da ba su da tushe, da kuma kokarin kara fahimtar juna da alaka a tsakanin kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments