Search
Close this search box.

Iran, Ta Yi Tir Da Kalamman Dan Majalisar Amurka Kan Amfani Da Bama-baman Nukiliya A Gaza

Iran ta yi Allah wadai da shawarar da wani dan majalisar dattawan Amurka na jam’iyyar Republican ya bayar cewa ya kamata Isra’ila ta yi amfani

Iran ta yi Allah wadai da shawarar da wani dan majalisar dattawan Amurka na jam’iyyar Republican ya bayar cewa ya kamata Isra’ila ta yi amfani da bama-baman nukiliya a Gaza.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Nasser Kan’ani a wani sako da ya fitar a ranar Talata a shafin X, ya ce wannan “mummuna” shawara kum abun tir da Allah wadai.

Shi dai dan majalisar na Amurka, Sanata Lindsey Graham, ya ce ya kamata Isra’ila ta yi “duk abin da ta ga ya dace wajen kai harin bam a Gaza, inda ya kwatanta lokacin da Amurka ta jefa bama-baman nukiliya a Japan a yakin duniya na biyu.

Graham ya kuma bukaci Shugaba Joe Biden da ya baiwa gwamnatin mamaya da karin bama-bamai.

“Wadannan munanan kalamai da dan majalisar dattijai na Amurka ya yi wajen bayar da hujja da karfafa gwiwar gwamnatin sahyoniyawan ta amfani da bama-baman nukiliya, na nuni da irin ta’asar da masu kunfan baki kan fafutukar hakkin bil’adama,” in ji Kan’ani.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yi kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye don nuna adawa da irin wadannan kalamai domin dakile ci gaba da bala’in jin kai da kisan kare dangi a zirin Gaza.

Jami’in na Iran ya kuma yi kira da a yi kakkausar suka a duniya kan irin goyon bayan da Amurka ke baiwa gwamnatin Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments