Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya yi gargadi ga kasashen Amurka da HKI wadanda suke son yayyanka kasashen musulmi a yankin kudancin Asiya don bawa HKI iko a kan yankin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran Al-Ghad a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kafin haka dai minister yana tare da shugaban kasar Iran Masoud Pazeskiyan don halattan taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashe musulmi 8 ta D-8 . Da farko dai ministan ya halarci taron ministocin kungiyar karo na 21th da kuma na shuwagabannin kasashen kungiyar ta 11th.
Ministan ya kara da cewa abinda HKI take yi a kasar Siriya na lalata makaman kasar, yana daga cikin al-amuran da Iran ta dade tana magana a kai. Kuma shi ne manufar Amurka da HKI ta yayyanka kasashen yankin zuwa kananan kasashe don bawa HKI karfi a kan dukkan kasashen yankin.
Daga karshe ministan yace HKI ta yi kokarin a baya don jawo yaki a tsakanin kasshen yankin don cimma wannan manufar.