Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-zargen Kasashen Turai Kan Shirinta Na Nukiliya

Iran ta yi watsi da zarge-zargen kasashen turai kan shirinta na nukiliya tare da shan slwashin mayar da martani kan wani mataki da suke gigin

Iran ta yi watsi da zarge-zargen kasashen turai kan shirinta na nukiliya tare da shan slwashin mayar da martani kan wani mataki da suke gigin dauka kanta.

Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga duk wani mataki kanta ta hanyar da ta dace.

M. Baghai na mayar da martani ne ga sanarwar hadin gwiwa da kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya suka fitar na zargin Iran da kasa mutunta alkawurran da ta dauka karkashin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 da kuma kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2231 da Amurka.

A matsayinta na mamba a hukumar IAEA, Tehran ta bayyana anniyarta ta yin hadin gwiwa da kuma yarjejeniyoyin da aka cimma yayin ziyarar da babban daraktan hukumar ya yi a Tehran a ranakun 14 da 15 ga watan Nuwamba.

Kasashe uku na Turai ba tare da yin la’akari da sakamakon ziyarar da babban daraktan ya kai ba, wanda zai iya zama tushen karfafa hadin gwiwa a nan gaba, sun ci gaba da tsare-tsarensu marasa ma’ana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments