Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya soki kwamitan tsaro na MDD saboda gazawarsa wajen kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza, saboda tana samun goyon bayan Amurka da kuma kasar Burtaniya. Wannan duk da cewa, kowa ya amince da cewa abinda HKI take yi a Gaza kissan Kiyashi ne wanda dokokin kasa da kasa suka haramta.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya ce ministan ya bayyana haka ne a ganawarsa da tokwaransa na kasar Siriya Bassam Assabbaag a birnin Damascus babban birnin kasar ta Siriya.
A ganawar ministocin biyu dai sun tattauna kan al-amura da dama daga ciki har da halin da ake ciki a yankin kudancin Asiya musamman a kasashen Falasdinu da Lebanon. Da kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Daga karshe ministocin sun bukaci kwamitin tsaro na MDD ya yi amfani da duk abinda yake da shi don kawo karshen kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza da kuma kasar Lebanon.