Iran Ta Yi Allawadai Da Kudurin Da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD Ta Amince A Kanta

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da hukumar ta yanke a kan JMI na son zuciya ne kuma saboda siyasar JMI a duniya ne. Bahraini ya kara da cewa, wannan hukuncin ya taba mutucin hukumar ta yin adalci ga wasu kasashen a duniya.

Bahraini ya kara dan cewa, abin mamakoi shigha ba’a taba jin wannan hukumar ta yankewa HKI irin wannan hukuncin ba, duk tare da cewa duk duniya tana ganin yadda take keta hakkin Falasdinawa tun shekara ta 2023.

Jakadan ya kara da cewa ‘sunan da hukumar ta bawa bincike da kuma hukuncinta wato (Kare Hakkin Bil’adama a JMI) da kuma sakamakon da ta fitar ya tabbatar da kariyar wannan hukumar, sannan ya zubar da mutuncin hukumar a idon kasashen duniya da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments