Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.
A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar su ka yi wa ma’aikatan hako ma’adanai dake yankin Harnai a arewacin gundumar ta Baluchestan.
Haka nan kuma ya ce, a duk inda ayyukan ta’addanci suke faruwa jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin Allawadai da shi.
Jami’in diplomasiyyar na Iran ya kuma jaddada bukatar ganin an kara samar da hadin kai a tsakanin Iran da kasar ta Pakistan a fagen fada da ayyukan ta’addanci.
A jiya Juma’a ne dai wani bom ya tashi da wata mota wacce take dauke da ma’aikatan hako ma’adanai a shahrag dake yankin Harnai.
Jami’an ‘yan sandan yankin na Baluchestan sun sanar da cewa ma’aikatar hako ma’adanai 11 ne su ka kwanta dama, yayin da wani adadi mai yawa nasu ya jikkata.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai wannan harin.
Sai dai a baya kungiyar nan ta ‘yan awaren yankin na Baluchestan mai suna Baluch Liberation Army ta rika daukar alhakin hare-hare irin wadannan.