Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Bakhae ya yabawa dan majalisar dokokin kasar Ireland Michael McNamara dangane da aibata kasashen turai yadda suka dulmuya kansu a cikin kissan kiyanshin da HKI take aikatawa a Gaza, da kuma yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a kansu don tabbatar da zaman lafiya da adalci a duniya, amma suka ki sauke shi.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Bakhae yana fadar haka a a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X, inda ya nakalto Michael McNamana ya ke yin tar da HKI kan kissan kiayshin da yake aikatawa a gazam da kuma rushe-rushen da kuma korar Falasdinawa da take a yankin yamma da kogin Jordan, haka ma da kissan da takewa masanan fasahar nukliyar kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya bayyana cewa, wannan matsayin da McNamara ya dauka shi ne yakamata kasashen turai su dauka, shi ne yakamata E3 da EU su dauka. Su yi tunanin yadda zasu samar da zaman lafiya a duniya, bas u harzukata ba.
Shi McNamara dai, dan majalisar dokokin kasar Ireland ne mai zaman kansa, kuma a cikin yan shekarun da suka gabata ya sha sukan HKI da kissan kiyashin da ta yi a gaza da kuma dirar mikiyan da take a yankin yamma da kogin Jordan.