Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga irin sadaukarwar da ‘yan jarida suka yi, wadanda suka rubuta irin wahalhalun da al’ummar Falastinu suke yi da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi a tsawon shekaru biyu da suka yi a zirin Gaza.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya rubuta a shafin sada zumunta na “X” a jiya Asabar cewa: Ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta tuna da jarumtakar ‘yan jarida da masu daukar hoto da suka sadaukar da rayukansu cikin shekaru biyu da suka gabata don bayyana hakikanin yakin da ake yi a Gaza da kuma fallasa irin kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suka yi wa Falasdinawa.
Baqa’i ya kara da cewa: A wannan karon, muna gaishe da kwararrun kafafen yada labarai sama da 200 wadanda suka rubuta irin wahala da radadin da Falasdinawan suke ciki, da kuma laifuffukan ‘yan mamaya, gami da shirin shafe wata al’umma daga kan doron kasa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take dauke da shi.