Iran Ta Shirya Fuskantar Siyasar Donald Trump Ta Sulhu Ko Gwgawarmaya

Shugaban Majalisar Muhimman Manufofi Na Siyasar Waje Ta Iran Kamal Kharrazi ya bayyana cewa, siyasar Donald Trump ba a fayyace take ba, amma dai Iran

Shugaban Majalisar Muhimman Manufofi Na Siyasar Waje Ta Iran Kamal Kharrazi ya bayyana cewa, siyasar Donald Trump ba a fayyace take ba, amma dai Iran ta shirya tattaunawa ko kuma yin gwgawarmaya. Kamal Kharrazi wanda tashar talabijin din “ almayadin” ta yi hira da shi, ya yi ishara da tarihin tsohuwar adawar Amurka da turai da jamhuriyar musulunci ta Iran, inda ya ce, tunaninsu na kifar da tsarin musulunci a Iran tsohon tunani ne ba sabo ba, tun farko-farkon cin nasarar juyi, kuma tunani ne da tsari da Amurka da Isra’ila suke da shi.

Kamal Kharrazi ya ce Iran Ta fuskanci adawa mai yawa tun daga kan kokarin kifar da tsarin musulunci, zuwa taimakawa Sadam Husain ya yaki Iran, sannan kuma takunkumai masu yawa,amma duk wadannan hanyoyin sun ci kasa daga ciki har da siyasar takunkumai masu tsanani –Ta Donald Trump.

Kamal Kharrazi wanda tsohon ministan harkokin waje ne, kuma a yanzu shugaban majalisar dake ayyana muhimman manufofi na siyasar waje ta Iran, ya kara da cewa; Domin fuskantar wadannan makirce-makirce, wajibi ne mu cigaba da zama masu karfi, domin babu abinda yake taka musu birki idan ba karfi ba. Wannan kuwa shi ne godaben da muke tafiya akansa, tun cin nasarar juyi, kuma makiya suna sane da cewa muna da karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments