Iran Ta Shiga Cikin Kasashe 10 A Duniya Masu Fasahar Samar Da Kayakin Yaki Don Amfanin Sojojin Sama

Mataimakin shugaban bangaren tsare-tsare a rundumar sojojin sama na JMI ya bayyana cewa JMI ta shiga cikin kasashe 10 a duniya wadanda suka mallaki fasahar

Mataimakin shugaban bangaren tsare-tsare a rundumar sojojin sama na JMI ya bayyana cewa JMI ta shiga cikin kasashe 10 a duniya wadanda suka mallaki fasahar samarwa sojojin sama na kasarsu makamai da kayakin aikin sojojin sama a duniya. Sannan  ‘makon kare kasa’ wata dama ce ta bayyana irin ci gaban da sojojin sama na JMI suka samu a wannan bangaren.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Air kwamanda Ali Akbar Talibzade yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a faretin ‘makon kare’ kasa wanda sojojin kasar suka gudanar a birnin Bushar na kudancin kasar a safiyar yau Asabar.

Talibzadeh ya kara da cewa sojojin kasar Iran tare da hadin kai da yan’uwansu na dakarun kare juyin juya halin musulunci wato IRGC sun zama abin alfahari ga kasar a sabbin ayyukan da suka aiwatar a masana’antar samar da makamai da kuma kayakin aikin sojojin sama a kasar.

Ya ce korewar sojojin sama na kasar ya kai ga suna iya gyaran jiragen yaki wadanda kasashen da suka samar da shi kawai suka iya gyaransu a baya. Sannan suna kera na’urori daban daban na jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa. Har sun shiga sahun kasashen na farko da suke samar da fasahar.

Talibzade ya godewa shugabancin jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae kan kekkyawar jagorancinsa musamman a fagen tsaron kasar wanda a halin yanzu ya kai ga kasar Iran ta shiga cikin kasashe masu fasahar kera manya manyan makamai da kuma kayakin aikin soje.

Daga karshe ya bayyana cewa birnin Bushar a yau ya zama kufar tsaron kasar Iran. Sannan ba’a barshi a baya ba a bangaren ci gaban tattalin arziki a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments