Iran Ta Sanar Da Nada Janar Jahanshashi A Matsayin Kwamandan Dakarun Rudunar Sojin Kasa

Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sunan brigadier janar Ali Jahanshashi a matsayin sabon kwamandan dakarun sojan kasar iran inda ya gaji brigadier janar

Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sunan brigadier janar Ali Jahanshashi a matsayin sabon kwamandan dakarun sojan kasar iran inda ya gaji brigadier janar Kiumars Haidari

Bayanan da yayi jim kadan bayan sanar da nadin nasa a yau Asabar, Jahanshahi ya jaddada cewa dakarun sojin kasar a shirye suke su mayar da martani kan duk wata barazana ta hanyar amfani da kwarewarsu da makamai na zamani da kuma daukan darasi kan rikicin da ya faru abaya bayan nan musamman yakin kwanaki 12 da Israila ta kallafa mata.

Haka zalika ya kara da cewa a halin yanzu sojoji sun bada fifiko ga kaidoji da dokoki guda 5 da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah imam khamnai ya sanya, wanda suka mayar da hankali kan iganta matakin kariya da karfin dan adam da nagarta da kayan aiki don mayar da martani kan duk wata barazana da za ta taso.

Daga karshe ya bayyana cewa bisa shiryarwar jagoran musulunci kan hadinkan alummar iran da karfin sojin kasar za’a iya murkushe duk wani makircin da makiya suke kullawa.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted