Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Korea Ta Arewa da kwallaye uku masu kyau a wasan da aka yi a filin wasa na “Azadi” na Tehran.
Kasashen biyu dai suna a karkashin; bangare na uku a Asiya saboda share fagen kai wa ga shiga gasar cin kofin kwallon duniya na 2026.
Dan wasa mai suna Muhammad Muhibbi ne ya ci kwallon farko, a mintuna 74 da fara wasan, sai kuma Mahdi Darimi a mintuna 77, sa Amir Husain Husain zadeh, a minti 3 da aka kara, bayan cikar mituna 90.
A bangaren kungiyar kwallon kafa ta Korea Ta Arewa kuwa, ta kammala wasannin nata da ‘yan wasa 10 bayan da aka kori daya daga cikinsu saboda adaidai mintuna na 66 daga fara wasa.
Sauran kungiyoyin da suke cikin wannan bangare na uku, da kuma su ka yi wasa a wannan rana, sun hada Uzbakistan da ta ci Qatar 3-0 a birnin Tashqand. Ita kuwa Kyrkizistan ta yi daya da daya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Iran ce a gaba a cikin bangaren nasu na uku; da take da maki 23, sai kuma Uzbakistan mai binta da maki 21, ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa tana da maki 15, yayin da Qatar take da maki 13. Kasar Kyrkizitan tana da maki 8, sai kuma Korea Ta Arewa mai maki 3.