Iran ta gabatar da makamai masu linzami da ta kera, inda ta nuna su a farkon makon tsaron kasa, inda kuma aka yi bikin kaddamar da wani sabon jirgin yaki mara matuki mai zango sama da kilomita 4,000.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, “An baje kolin makaman ballistic 23 a ranar Asabar, wadanda suka hada da makamai masu linzami na Kheibar Shekan 2, makamai masu linzami na Fateh 2, makamai masu linzami na Haj Qasem 4, makamai masu linzami na Qadr H 2, makaman Emad 2, makamai masu linzami na Khorramshahr 3, makamai masu linzami na Sejil 4 da na Jihad 4.” .
Makami mai linzami samfurin Jihad dai shi ne na baya-bayan nan da rundunar sojojin sama ta IRGC ta samar, wanda aka nuna a karon farko a faretin makon tsaron kasa.
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kuma gabatar da samfurin Shahed-136B, sabon samfurin jirgin yaki mara kamikaze samfurin Shahed-136 a karon farko.
An baje kolin sabbin kayyakin na soji ne a makabartar marigayi Imam Khumaini da ke kudancin Tehran. An gudanar da fareti a ranar farko ta makon tsaron kasa, wanda zai ci gaba har zuwa tsawon mako guda a nan gaba.
A kowace shekara ana gudanar da irin wannan fareti, tare da nuna sabbin kayyayakin yaki, da sauran kayan aiki na soji da Iran ta samar a cikin shekara.