Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi.

Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud.

Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama  a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko da Afghanistan a shekarar 2021.

Kasashen biyu makwabtan juna  sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Doha a ranar 19 ga Oktoba a zagaye na farko na tattaunawar zaman lafiya wanda Qatar da Turkiyya suka shiga tsakani.

Duk da haka, zagaye na biyu na tattaunawar a Istanbul ya ƙare ba tare da cimma wani abin azo a gani ba.

Bangarorin biyu sun fara zagaye na uku na tattaunawar zaman lafiya a Istanbul a ranar Alhamis, amma tattaunawar ta wargaje washegari.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Afghanistan, ya yaba wa Iran kan wannan batu, sannan ya yi karin bayani kan halin da ake ciki da kuma sakamakon tattaunawar da aka yi tsakanin Kabul da Islamabad.

Muttaqi ya sake nanata kudurin Afghanistan na amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma warware matsalolin ta hanyar diflomasiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments