Iran Ta Musanta Zargin Nethalands Na Cewa Tana Da Hannun A Kokarin Kisa A Kasar

Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu

Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu a shekarar da ta gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tace Ofishin jakadancin Iran da ke Netherlands  ta fidda wannan sanarwan ne a jiya Alhamis. Ta kuma kara da cewa, kasar Iran wacce ta fi ko wace kasa a duniya fama da yan ta’adda, ba za ta yi kokarin kasashe wani a wani wuri ba.

Sanarwan ta bayyana cewa wannan al-amarin siyasace ta tsakanin jami’an siyasa na kasar ta Netherlands  don neman amincewar masu kuri’a.

Kafin haka dai wata cibiyar ayyukan tsaro ta kasar Netherlands  mai suna AIVD ta bada rahotomta na shekara shekara kan abinda ya shafi ayyukan ta’addancin inda ta ammabi kasar Iran a ciki.

Har’ila yau wannan rahoton yasa ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Netherlands  ta kira jakadan JMI a kasar zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don gabatar da korafinta.

Gwamnatocin kasashen Turai musamman kasar Faransa tana gudanar da taron yan adawa da JMI a kasashensu, wadanda kuma sune suka kashe Iraniyawa da dama a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments