Iran Ta Musanta Zargin Amurka Kan Cewa Kungiyoyi Masu Fada Ha HKI Suna Daukar Umurni Daga Wajenta Ne

Jakadan kasar Iran a MDD Amir Sa’eid Iravani ya musanta zargin kasar Amurka na cewa falasdinawa dauke da makamai a Gaza suna aiki ne tare

Jakadan kasar Iran a MDD Amir Sa’eid Iravani ya musanta zargin kasar Amurka na cewa falasdinawa dauke da makamai a Gaza suna aiki ne tare da umurnin Iran. A kuma dukkan yankunan da HKI take mamaye da su a kasar Falasdinu da ta mamaye.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Iran vani yana cewa Amurka ta dorawa iran wannan zargin ne saboda boye laifukan yakin da HKI take aikatawa a Gaza da kuma sauran yankunan Falasdinawa da take mamaye da su.

A wani jawabin da ta gabatar a gaban kwamitin tsaro na MDD a ranar Laraba mai rike da mukamin jakadan Amurka a MDD Dorothy Shea ta bayyanawa kwamitin tsaro kan cewa dole kungiyar Hamas ta mika makamanta sannan da ita da sauran Falasdinawa su bar Gaza su je inda suka ga dama.

Bayan jawabinta ne Iravani ya rbutawa babban sakataren MDD da kuma shugaban kwamitin tsaro na wannan wato Carolyn Rodrigues-Birkett  wasika inda yake musanta zarge zargen na Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments