Iran ta lashi takobin daukar mataki kan takunkumin Birtaniya, Faransa da Jamus

Iran ta karyata rahotannin da ke cewa ta mika makamai ga Rasha domin da Ukraine, inda ta ce wanann farfaganda  ce ta karya da yaudara,”

Iran ta karyata rahotannin da ke cewa ta mika makamai ga Rasha domin da Ukraine, inda ta ce wanann farfaganda  ce ta karya da yaudara,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani.

Kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya sun kakaba wa Iran sabbin takunkumai, bisa zargin cewa kasar ta kai wa Rasha makamai masu linzami da za ta yi amfani da su a yakin Ukraine.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewa, Iran ta kara yawan  goyon baya na soji da ake zargin ta na baiwa kasar Rasha, lamarin da ke zama barazana kai tsaye ga tsaron Turai.

Haka kuma, sun ce a halin yanzu sun sami “tabbacin” cewa Iran ta yi jigilar irin wadannan makamai.

Sakamakon haka kasashen Turai za su soke yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama da aka kulla da Iran Air. Har ila yau, sun sanar da wani shiri na ayyana wasu muhimman hukumomi da daidaikun mutane da ke da hannu a shirin makamai masu linzami na Iran da kuma zargin cewa suna hannu wajen mikawa kasar Rasha makamai.

Kasashen Turai uku sun fitar da sanarwar ne duk da ci gaba da musanta zargin da Iran ke yi na baiwa Rasha makamai domin amfani da su a Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments