Iran Ta Cilla Tauraron Dan’adam Mafi Nauyi Mai Suna ‘Saman 1’ Zuwa Sararin Samaniya Tare Da Samun Nasara

Masana a ma’aikatar tsaron kasar Iran sun sami nasarar aika tauraron dan’adam mafi nauyin wanda kasar ta taba aikawa zuwa sararin samania a safiyar Jaumma’a

Masana a ma’aikatar tsaron kasar Iran sun sami nasarar aika tauraron dan’adam mafi nauyin wanda kasar ta taba aikawa zuwa sararin samania a safiyar Jaumma’a tare da samun nasara.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya kara da cewa nauyin abinda rokan ‘Simorg’ ta dauka a wannan karon ya kai kilogram 300. Kuma shi ne kaya mai nauyi mafi yawa, wanda aka taba cillawa zuwa sararin samaniya a kasar.

Labarin ya kara da cewa tauraron ‘Saman na 1, ya isa inda ake son ya isa a sararin samaniya mai nisan kilomita 410, kuma ya hau kan falakin da ake son ya hau.

Banda haka tauraron Saman na 1 wanda aka kera a cikin gida yana da kayan aiki kara nisansa daga doron kasa.

An fara amafani da tauraron saman ne a cikin watan fabrairun shekara ta 2017 a lokacinda shugaban kasa na lokacin, Dr Hassan Rauhani ya gabatar da shi, a wani bukin da aka gudanar a ranar sararin samaniya ta kasa.

Sannan kumbon ‘Simorgh’ kuma, kumbo ne wanda yake daukar taurarin dan’ dam da wasu kayaki, zuwa sararin samaniya wanda kuma yake amfani da makamashi na ruwa-ruwa, mai kashi kashi biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments