Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su.
Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya.
Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu kaiwa hare-hare a HKI, hatta kan wurarenda wadanda HKI ta boye su, suna hannu, kuma zata sha mamaki idan ta kuskura ta takali Iran da yaki.
Dangane da dimbin bayanan sirri da kasar ta samu kuma, majaliasar ta kara karfafa shirin kare kasar daga HKI saboda samunsu.
Har’ila yau suna da cikakkun bayanan wuraren da zasu kaiwa hari, gwagwadon wauraren da HKI ta taba a cikin kasar Iran.