Iran Ta Ce : Wasu Bangarorin Kasashen Waje Suna Kokarin Mamaye Yankunan Kasar Siriya

Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Wasu bangarorin kasashen waje a Siriya suna kokarin mamaye yankunan kasar da kuma rarrabata

Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Wasu bangarorin kasashen waje a Siriya suna kokarin mamaye yankunan kasar da kuma rarrabata

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci a Iran Manjo Janar Hussein Salami ya bayyana cewa: Wasu bangarorin kasashen waje da ke kasar Siriya na neman raba kasar ta Siriya, kuma kowanne daga cikinsu na neman mamaye wasu yankunanta.

Manjo Janar Hussein Salami ya kara da cewa: Kasashen waje na neman mamaye kasar Siriya. Yahudawan sahayoniyya sun mamaye kudancin kasar, wata runduna ta mamaye arewacin kasar, sannan ta uku kuma ta mamaye gabashin kasar ta Siriya.

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Ba su je Siriya domin mallake ta ba, ko kuma neman muradun fadada manufofinsu ba, a’a sun je ne domin kare martabar al’ummar musulmi.

Manjo Janar Hussein Salami ya ci gaba da cewa; Al’ummar Siriya na fuskantar makoma maras tabbas, kuma zasu gane kimar gwagwarmaya da kuma gane cewa abin alfaharinsu yana cikin ci gaba da kasancewar kasar, kasa daya dunkulalliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments