Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki.

Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman Amurka ba su tuhumi Iran da kokarin mallakan makaman Nukliya ba, sai dai suna nufin tursasawa kasar ne, don ta mika kai garesu a kan dukkan al-amura.

Imam Khaminai ya kara da cewa, da Iran za ta mika kai dangane da shirinta na makamashin nukliya, da gobe kuma zasu ce, yaya batun makamanki masu linzami idan ta amin ce, sai su kawo batun siyasarta a gabasa ta tsakiya da sauransu. Don  haka bukatunsu ba za su kare ba sai sun mamaye kasar gaba daya.

Ministan ya kammala da cewa, tattaubawan ta Trump yake kiran Iran zuwa gareshi tursasawa ne. idan da tana batun tattaunawa ne, da gaske. To da yarjeniyar JCPOA ya wadatar. Sai tunda wani abu ne daban, take amfani da tursasawa, wanda kuma yake iya kaiwa ga yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments