Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana matsayin kare haƙƙin ɗan Adam a wurin Amurka da yahudawan sahayoniyya a matsayin fuskoki biyu na kwandala guda
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya rubuta a shafin dandalin X cewa: Sakamakon binciken da tashar talabijin ta CNN ta kasar Amurka ta gudanar yana nuni da cewa: Sojojin yahudawan sahayoniyya suna azabtar da fursunonin Falasdinu a wani wurin da ake tsare da Falasdinawan a asirce a saharar Negev da ke kudancin haramtacciyar kasar Isra’ila. Yayin da sojojin Amurka suka tsare fursononi suka dinga azabtar da su a tsibirin Guantanamo da gidan kurkukun Abu-Ghuraib.
Don haka Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Yaudarar da Amurka da yahudawan sahayoniyyar suke yi a fagen kare hakkin dan Adam tana matsayin fuska guda ne kamar yadda fuskoki biyu na kwandala guda yake.