Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai dangane da haka da zarar an tantance lokaci da wuri.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Har yanzu ba a sanya ranar karshe da za a gudanar da shawarwarin na gaba ba, amma ana duban shawarar da Oman ta gabatar na gudanar da tattaunawar a farkon mako mai zuwa.