Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, Iran na dora alhakin kai hare-hare ba bisa ka’ida ba kan cibiyoyin nukiliya a kan Amurka da Isra’ila.
“Ba shakka muna la’akari da gwamnatin Isra’ila da Amurka a matsayin masu alhakin hare-hare a kan cibiyoyin nukiliya na Iran,” in ji Esmaeil Baqaei yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da wakilin kamfanin illancin IRNA ya tambaye shi kan furucin na baya-bayan nan da Sakatare Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi ya yi, wanda ya ce bai ce Iran na kokarin kera makaman nukiliya a cikin rahotannin da ya bayar ba, a wani yunkuri na wanke kansa daga tuhumce-tuhumce kan harin da sojoji suka kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran.
Baqaei ya ce, duk da haka, rahoton hukumar ta IAEA da kuma yin watsi da doka da ka’idoji daga bangaren Amurka da kasashen Turai uku suka yi, ya samar da wata hujja ga Isra’ila da Amurka na yin amfani da hakan domin aiwatar da ayyukan wuce gona da iri.
Ya yi nuni da cewa, ko da shugaban hukumar ta IAEA ya yarda cewa babu wani rahoto daga hukumar ta IAEA da ke nuni da cewa shirin nukiliyar Iran ya kauce daga tafarkin zaman lafiya, A irin wannan yanayi, ana sa ran hukumar IAEA za ta gaggauta yin Allah wadai da matakin da Isra’ila da Amurka ke dauka kan cibiyoyin nukiliyar Iran, in ji shi.