Iran ta ce a shirye take ta tallafa wa Burkina faso a yakin da take da ta’addanci.
Wannan bayyanin ya foto ne bayan wata ganawa tsakanin Firaministan Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouédraogo da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Burkina Faso, Mista Mojtaba Faghihi a Ouagadougou.
Taron dai ya baiwa mutanen biyu damar sake yin nazari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu.
A cikin wannan yanayi, Iran ta bayyana aniyar ta na tallafawa Burkina Faso, a kokarinta na dakile matsalar rashin tsaro.
Tehran, ta bakin jakadanta, ta kuma bayyana sha’awarta kan sauran fannonin hadin gwiwa, kamar su noma, masana’antu, likitanci da al’adu.
Ya ce Iran a shirye take ta ba da dukkan goyon bayan da ya dace ga Burkina Faso, yana mai jaddada a shirye Tehran ta ke na mara wa Ouagadougou baya a yakin da take yi da ta’addanci.
Wannan furuci na zuwa ne a wani yanayi da Burkina Faso ke fuskantar matsalar rashin tsaro, tana neman karkata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Firaministan Burkina Faso ya yi marhabin da wannan shiri, yana mai jaddada matsayin kasarsa da kokarin Iran wajen yaki da ta’addanci.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Wannan taron ya ba da damar tattaunawa kan yadda za a yi hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da noma, masana’antu, likitanci da al’adu, wanda ke nuna muradin karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.