Jakadan kasar Irana kasar Netherlands, Hadi Faraj-vand ya yi kira ga kutun kasa da kasa ta ICC ta hukunta wadanda suka aikata laifuffukan yaki a duniya, ba tare da shigar da harkokin siyasa, bangaranci da kuma fuska biyu a hukluncinta ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Hadi Faraj-vand wanda ya gabatar da jawabi a taron kasashe wadanda suka amince da yarjeniyar Roma karo na 23 yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin HKI, banda kissan kare dangin da take wa Falasdinawa a Gaza, ta rusa gine-ginen MDD da dama a zirin gaza, ta rusa wuraren ibada wadanda suka hada da masallatai da kuma coci-coci. Har’ila yau da asbitoci, da kuma dukkan gine -gine masu muhimmanci ga falasdinawa.
A ranar 21 ga watana Nuwamban da yagabata ne kotun ta ICC ta fidda sammacin kama Firay ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministansa na yaki Yoav Galantz. Tare da tuhumarsu da aikata laifukan yaki da kuma amfani da yuwan a matsayin makami kan falasdinawa a Gaza a cikin shekaran da ta gabata.